Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Dole ne Afirka ta samu wakilci a kwamitin sulhu na MDD- Ramaphosa

Shugaban Kasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa ya ce ya zama dole nahiyar Afirka ta samu wakilci a Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya domin nunawa duniya cewar kowanne yanki na da wakilci a ciki.

Shugaban Kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa kuma shugaban kungiyar tarayyar Afrika AU.
Shugaban Kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa kuma shugaban kungiyar tarayyar Afrika AU. REUTERS/Sumaya Hisham/File Photo
Talla

Yayin da ya ke gabatar da jawabin sa a Majalisar ta bidiyo, shugaban ya ce a dai dai lokacin da Majalisar ke bikin cika shekaru 75 da kafuwa, ya zama wajibi su dada bayyana bukatar su ta ganin nahiyar Afirka ta samu wakilcin da ya dace a kwamitin sulhun domin bayar da damar tattaunawa a matsayin koli cikin sauki.

Ramaphosa ya ce ta hanyar sake fasalin Majalisar ne kawai za a samu damar shawo kan wasu daga cikin dadaddun matsaloli da suka addabe ta.

Shugaban wanda ya ke jagorancin kungiyar kasashen Afirka ta AU ya kuma bukaci dakatar da biyan basussukan da ake bin kasashen Afirka saboda illar da annobar korona ta musu, ganin yadda annobar ta hana gudanar da ayyukan cigaba sakamakon yadda kasashen suka karkata kasafin kudin da suka yi domin tinkarar kula da lafiya da samar da ruwan sha da gidaje da ilimi zuwa yaki da annobar.

Ramaphosa ya kuma bukaci kara kaimi wajen yaki da cin hanci da rashawa wanda ya ce yana hana al’ummar nahiyar samun bukatun da ya dace da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.