Isa ga babban shafi
Afrika

Shugabannin Afrika da suka manne kan karagar mulki

Shugabannin kasashen Guinea da Cote d’Ivoire Apha Conde da Alassane Ouattara duk sun bayyana aniyarsu ta sake takarar neman wa’adi na 3, abin da ya saka su cikin jerin shugabannin Afrika da suka sauya kundin tsarin mulki domin ci gaba da zama a karagar mulki.

Wasu daga cikin shugabannin kasashen Afrika a taron Ecowas.
Wasu daga cikin shugabannin kasashen Afrika a taron Ecowas. CNN.com
Talla

Daga cikin ire-iren wadannan shugabannin da suka sauya kundin tsarin mulkin kasashensu, akwai Azali Assoumani na kasar Comoros, wanda ya sauya kundin kasar a shekarar 2018, sai Paul Kagame na Rwanda a shekarar 2017, abin da zai ba shi damar ci gaba da mulki har zuwa 2034.

A 2015, shugaba Denis Sassou Nguesso na Congo ya aiwatar da sauyin kuma aka sake zaben sa a 2013 domin yin wa’adi na 3, sai kuma shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe wanda ya sauya kundin a  2013, sannan ya lashe zaben kasar ya kuma ci gaba da mulki har zuwa shekarar 2017 da aka kore shi daga karagar mulki.

Majalisar Dokokin Djibouti ta amince da shirin yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyara a  2010, abin da ya bai wa shugaba Ismael Omar Guelleh da ke kan karaga tun daga shekarar 1999 damar ci gaba da zama a karagar mulki, kuma ya samu nasara a zaben 2011 da 2016.

Sai Kamaru inda shugaba Paul Biya ya sauya kundin tsarin mulki a  2008, ya kuma cire wa’adin mulki, abin da ya ba shi damar ci gaba da zama a karagar mulkin da ya fara tun shekarar 1982, kuma yanzu haka yana wa’adi na 7.

Shugaba Yoweri Museveni na Uganda ya sauya kundin tsarin mulkin kasar a shekarar 2005, inda aka cire wa’adin shugabancin kasar, abin da ya bai wa shugaban wanda ya hau karagar mulki a shekarar 1986, damar sake tsayawa takara a zaben da za ayi a badi.

Shugaba Idris Deby na Chadi da ya karbe iko a shekarar 1990 ya sauya kundin tsarin mulkin kasar a  2005, kuma a shekarar 2016 aka zabe shi a kan wa’adi na 5.

A kasar Togo, an sauya kundin tsarin mulkin kasar a 2002 domin bai wa shugaban kasa damar ci gaba da zama a karagar mulki ba tare da kayyadewa ba, abin da ya bai wa shugaba Gnassingbe Eyadema da ya hau karaga a 1967 damar ci gaba da mulki, kuma lokacin da ya mutu ‘dansa Faure Gnassingbe ya gaje shi, kuma yanzu haka yana wa’adi na 4.

Bayan wadannan kasashe da suka samu nasarar sauya kundin tsarin mulkinsu, akwai wasu kasashen da suka yi yunkuri amma kuma ba su samu nasara ba.

Daga cikinsu akwai Burkina Faso, wanda yunkurin sauya kundin ya haifar da kazamar zanga-zangar da ta kifar da gwamnatin shugaba Blaise Compaore a shekarar 2014, sai kuma Zambia, inda al’ummar kasar ta tilasta wa shugaba Frederik Chiluba sauya matsayinsa na yi wa kundin gyara a shekarar 2001.

A shekarar 2002, Majalisar Dokokin Malawi ta ki amincewa da bukatar shugaba Bakili Muluzi na sauya kundin domin yin wa’adi na 3, yayin da Burundi ta fada rikici a shekarar 2015 lokacin da shugaba Pierre Nkurunziza ya ce zai tsaya wa’adi na 3 abin da ya kai ga mutuwar mutane sama da 1,200.

A Jamhuriyar Nijar shugaba Muhammadu Tandja ya sauya kundin amma sojoji suka kifar da gwamnatinsa, yayin da Majalisar Dokokin Najeriya ta ki amincewa da bukatar shugaba Olusegun Obasanjo na sauya kundin tsarin mulkin kasar domin ba shi damar yin wa’adi na 3.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.