Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

Ma'aikatar tsaron Najeriya ta ce ba sojoji ne suka kai wa gwamnan Borno hari ba

Ma'aikatar Tsaron Najeriya tace mayakan Boko Haram suka kai hari kan tawagar motocin Gwamnan Jihar Barno, Babagana Umara Zulum sabanin ikIraninsa cewar sojoji suka kai masa hari a makon jiya, lokacin da ya kai ziyara Baga dake karamar hukumar Kukawa.

Babban Hafsan rundunar sojin Najeriya Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai.
Babban Hafsan rundunar sojin Najeriya Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai. AFP PHOTO/STRINGER
Talla

Manjo Janar John Enenche dake Magana da yawun dakarun dake aiki a fagen fama yace binciken da suka gudanar a inda aka kai harin ya nuna cewar Boko Haram ta kaddamar da harin.

Janar Enenche yace ganin zargin na Gwamnan na da girma sosai ba su bata lokaci wajen gudanar da bincike a kai ba, kuma bayanan da suka tattara ya tabbatar musu cewar babu hannun wani soja cikin wadanda suka kai harin.

Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron ya ce sun bi matakai da dama wajen tabbatar da wannan matsayi da suka hada da bidiyon da aka dauka lokacin harin da inda aka dinga jin karar harbe harben da kuma irin makaman da aka yi amfani da su wajen kai harin da suka sha banban da na sojin.

Janar Enenche ya ce babu gaskiya kan zargin da aka yi wa dakarun nasu dake sadaukar da rayukan su domin kare lafiyar jama’a.

Idan dai ba’a manta ba, Gwamna Zulum ya zargi sojin Najeriya da kai masa hari lokacin da ya kai ziyara domin ganin halin da jama’ar sa ke ciki a Baga, inda yake cewa ba zai cigaba da nade hannun sa yana kallon mutanen sa na fuskantar ukuba ba, yayin da wasu ke yiwa kokarin su zagon kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.