Isa ga babban shafi
Najeriya

Mutane 10 sun mutu sakamakon kifewar kwale kwale a Najeriya

Mutane goma sun mutu, an ceto biyar, yayin da wasu hudu suka bace, sakamakon kifewar wani kwale kwalen daukar fasinja a birnin Lagos na Tarayyar Najeria, kamar yadda hukumomi suka bayyana a Asabar din nan.

kananan jiragen ruwa a gabar ruwan Lagos, Najeriya.
kananan jiragen ruwa a gabar ruwan Lagos, Najeriya. REUTERS/Temilade Adelaja
Talla

Sanarwa daga hukumar kula hanyoyin ruwan jihar Lagos a Najeriya ta ce, kwale kwalen yana kan hanyarsa ta zuwa Badagry ne daga gidan yarin Kirikiri a tsakiyar mako, kwatsam sai igiyar ruwa ta mai dabibaiyi.

Sanarwar ta ce jimillar mutane 19 ne a cikin cikin kwale kwalen da wannan iftila’i ya afka wa, kuma aka yi rashin sa’a akasarin fasinjojin da ke ciki ba sa sanye da rigar kariya.

Hukumar kula da hanyoyin ruwan ta kama matukin jirgin ruwan, kuma ta mika shi ga ‘yan sandan da ke kula da sufurin ruwa don ci gaba da bincike, da kuma hukunci.

Hatsarin kananan jirage ruwa a Najeriya dai ba wani bakon abu bane, kuma yana faruwa ne sakamakon daukar fasinjoji da kaya fiye da kima da masu harkar suke yi, da kuma rashin bin ka’aidojin kiyaye haddura.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.