Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

'Yan bindiga sun kashe mutane 20 a Dafur

A karon farko cikin shekaru da dama ‘yan bindiga sun kashe mutune 20, ciki har da yara kanana a yankin Dafur na kasar Sudan ta Kudu da yaki ya daidaita.

'Yan bindiga sun harbe mutane 20 a Dafur har lahira.
'Yan bindiga sun harbe mutane 20 a Dafur har lahira. Daily Post
Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito wani mazaunin yankin yana cewa duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka yi ne wannan lamari da ya rutsa da mutanen har da mata biyu da kananan yara ya auku.

A shekarar 2003 ne rikici ya barke a yankin Dafur tsakanin kabilu ‘yan tsiraru da ‘yan tawaye masu biyayya ga tsohon shugaban Sudan Omar Hassan al-Bashir .

Rikicin na yankin ya yi sanadin mutuwar mutane dubu 30, kana ya raba miliyan 2 da rabi da muhallansu, a cewar majalisar dinkin duniya.

A watan Afrilun shekarar da ta gabata ne aka hambarar da gwamnatin shugaba al-Bashir, biyo bayan watanni da aka kwashe ana zanga zangar kin jinin jagorancinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.