Isa ga babban shafi

Tanzania na zaman makoki saboda mutuwar Mkapa

An shiga zaman makoki na mako daya sakamakon rasuwar tsohon shugaban Tanzania Benjamin Mkapa, yayin da shugabanin kasashe ke ci gaba da aikewa da sakwannin ta’azziya.

Tsohon shugaban Tanzania Benjamin Mkapa.
Tsohon shugaban Tanzania Benjamin Mkapa. MWANZO MILLINGA / AFP
Talla

Tsohon shugaba Mkapa ya rasu ne a ranar Alhamis cikin dare zuwa wayewar garin wannan Juma’a yana da shekaru 81 a duniya a wani asibitin Dar-es-Salam kamar dai yadda wata sanarwa daga fadar gwamnatin kasar ta tabbatar.

Marigayi Mkapa ya mulki Tanzania daga shekarar 1995 zuwa 2005, sannan yana daga cikin mutanen da ake ganin cewa sun taka gaggarumar rawa don tabbatar da zaman lafiya a yankin gabashin Afrika, kuma a  lokacin mulkinsa, an shaidi ya gina tattalin arzikin Tanzania.

Daga cikin fitattun mutanen da suka nuna alhini game da rasuwar Mkapa har da madugun ‘yan adawar Kenya Raila Odinga da wasu fitattun mutane da dama daga Afrika.

Kafin rike nasarar darewa kan karangar shugabancin kasar, marigayi Mkapa ya rike mukamin Ministan Harakokin Wajen Tanzania, ya kuma rike mukamin Jakadan kasar a Amurka da kuma Ministan Ilimi mai zurfi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.