Afrika
Shugabannin Afrika za su yi tattaunawar sulhu a Mali
Shugabannin kasashen Afrika 5 na kan hanyarsu ta zuwa Bamako na kasar Mali domin shiga tattaunawar sulhu da ake ci gaba da yi a kasar.
Wallafawa ranar:
Talla
Shugabannin 5 sun hada da na Ivory Coast da Ghana da Senegal da Nijar, wadanda ake sa ran su shiga tattaunawar a Bamako a ranar Alhamis.
Shugaban Mali Boubakar Keita na fuskantar matsin lamba tun watan jiya daga masu bore da ‘yan adawa da ke neman ya yi murabus saboda rashin tsaro da matsalar cin hanci da gazawa wajen tada komadar tattalin arzikin kasar.
Mutane 11 aka tabbatar da mutuwarsu saboda boren ya zuwa yanzu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu