Musayar makamai da shanu a Zamfara
Gwamnan Zamfara dake Najeriya, Bello Matawalle, ya yi alkawarin bayarda shanu biyu a matsayin musaya ga duk dan bindigar da ya mika bindigarsa ta AK47 a jihar.
Wallafawa ranar:
Gwamna Matawalle ya bayyana haka ne a alhamis din nan, lokacin da ya karbi bakuncin babban sufeton ‘yan sandan Najeriya Muhd Adamu da kuma shugaban hukumar jami’a tsaron farin kaya na DSS Yusuf Bichi.
Gwamnan Zamfaran, yace samun nasarar shirin afuwar zai kawo karshen matsalar hare-haren ‘yan bindigar a jihar da ma makwabtan ta, zalika zai karfafa tattalin arzikin wadanda suka ajiye makaman, ta hanyar neman halaliyarsu cikin ruwan sanyi, sai dai Bello Matawalle ya ce ba za bari ‘yan bindigar da suka tuba su sake koma cikin dazuka da sunan zama ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu