Isa ga babban shafi
Afrika-Tattalin arziki

Kasashe masu fitar da mai a Afrika za su tafka asarar dala biliyan 34- IMF

Asusun bada lamuni na IMF ya wallafa wani sabon rahoto da ya yi hasashen cewar Najeriya da sauran kasashe masu arzikin manfetur a nahiyar Afrika za su tafka hasarar kudaden shigar da ya kamata su samu daga fannin danyen man da ya kai dala biliyan 34, a dalilin tasirin annobar coronavirus.

Wata matatar man fetur a Libya.
Wata matatar man fetur a Libya. AFP/Abdullah Doma
Talla

Rahoton asusun na IMF ya ce wani sabon kalubalen da kasashen na Afrika za su fuskanta musamman masu arzikin danyen man fetur, shi ne takurewar kasafin kudadensu da kuma sabon nauyin basukan makudan kudade kari kan wadanda suka yi musu katutu a baya kafin bakewar annobar COVID-19.

Asusun IMF ya kara da cewar bincikensa ya nuna tun bayan faduwar farashin danyen mai a duniya da aka gani a shekarar 2014, ayyukan masana’antu da na raya kasa da kuma zuba hannayen jari na ci gaba da fuskantar koma baya a mafi akasarin kasashen Afrika dake fitar da danyen mai zuwa kasuwannin duniya.

IMF ya dora alhakin fuskantar mastsalar kan gazawar gwamnatoci wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu, da kuma matsalolin tsaro a kasashe da dama, musamman a Najeriya da Libya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.