Isa ga babban shafi
ECOWAS-Mali

ECOWAS ta nemi sake gudanar da zaben Mali da ya haifar da rikicin siyasa

Kungiyar ECOWAS ta bukaci Mali ta sake gudanar da wasu daga cikin zabukan sassan kasar da sakamakonsu ya tunzura al’umma wanda ya kai ga zanga-zangar bukatar murabus din shugaba Boubacar Keita a Juma’ar da ta gabata.

Wasu masu zanga-zangar adawa da shugaba Ibrahim Boubacar Keita a Mali.
Wasu masu zanga-zangar adawa da shugaba Ibrahim Boubacar Keita a Mali. REUTERS/Matthieu Rosier
Talla

Sanarwar da ECOWAS ta fitar ta bukaci gwamnatin kasar ta Mali ta sake duba na tsanaki ga sakamakon zabukan na dukkanin yankuna da sassan kasar tare da sabunda wasu daga ciki don kawo karshen rikicin siyasar da hakan ya haifar.

Bukatar ta ECOWAS na zuwa kwana guda bayan Sakatare Janar na Majlisar Dinkin Duniya Antonio Gutteress ya bukaci bangarorin adawa suja hankalin magobaya bayansu don dorewar zaman lafiya a kasar mai fama da rikici tsawon shekaru 8.

Dubun dubatar al’ummar kasar ta Mali ne dai suka gudanar da wata kakkarfar zanga-zangar adawa da gwamnati a Juma’ar da ta gabata, bisa bukatar murabus din shugaban wanda ke tsaka da wa’adinsa na biyu a mulkin kasar bayan zabensa a 2018.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.