Isa ga babban shafi

Ana tuhumar sojojin Kamaru 3 da kissan gilla

Kutu a Kamaru ta tuhumi wasu sojoji 3 da zargin kisan kai sakamakon rawa da suka taka a wani kissan gilla a yammacin kasar, inda jami'an tsaro ke fafatawa da ‘yan aware masu dauke da makamai.

Wani sojan Kamaru a kan iyakar kasar da Najeriya
Wani sojan Kamaru a kan iyakar kasar da Najeriya Reuters
Talla

Kakakin ma’aikatar tsaron kasar Kanal Cyrille Atonfack Guemo, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran APF cewar, tuni aka tisa keyar sojojin uku gidan yari a birnin Yaounde.

Ana zargin dakarun tsaron Kamaru da bude wuta kan fararen hula a kauyen Ngarbuh dake arewa maso Yammacin kasar a ranar 14 ga watan Fabarairu wannan shekara ta 2020, inda akalla kananan yara 10 da mata 3 suka rasa rayukansu, a cewar hukumomi, saidai Majalisar Dinkin Duniya tace fararen hula akalla 23 aka kashe.

Da farko dai rundunar tsaron Kamaru ta musanta alhakin kisan na kiyashi, inda tace hadarin tankunan mai ne suka haddasa kissan yayin dauki ba dadi sakaninta da mayakan ‘yan aware.

Bayan matsin lamba daga kungiyoyin kare ‘yancin bil’adama da manyan kasashen duniya, shugaban kasa Paul Biya ya bada umurnin gudanar da bincike dangane da kissan.

Rikici tsakanin soji da mayakan ‘yan aware masu neman ballewa don kafa jamhuriyar Ambazonia a yankunan Arewa maso yamma da Kudu maso Yammacin kasar da ake amfani da Turancin Inglishi, ya yi sanadiyar rayukan sama da mutane dubu 3, yayin da sama da dubu 700 suka tsere daga muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.