Isa ga babban shafi
Kamaru

CPJ ta bukaci bincike kan kisan Wazizi

Kungiyar kare hakkin ‘yan jaridu ta duniya CPJ, ta bi sahun wasu takwarorinta na kare hakkin 'yan jaridu da na 'yan cin bil'adama 9 wajen kira ga gwamnatin Kamaru da ta amince a gudnadar da sahihin bincike dan gano musababbin mutuwar dan jarida kasar Samuel Wazizi da ya mutu a hannun jami’an tsaron Kasar.

Samuel Wazizi dan Jaridar Kamaru da ya mutu a hannun jami'an tsaro.
Samuel Wazizi dan Jaridar Kamaru da ya mutu a hannun jami'an tsaro. CPJ
Talla

Cikin wata sanarwa da ta fitar Laraban nan, kungiyar CPJ, tayi  kira ga Mambobin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da su yi amfani da damar taron da zasu  gudanar da ofishinsu kwamitin na Yankin Tsakiyar Afrika, a ranar 12 ga watan Yunin nan da muke ciki, wajen ganin gwamnatin Kamaru ta amince a gudanar da sahihin binciken don gano musababbin mutuwar dan jaridar Samuel Wazizi.

Binciken da kungiyar ta CPJ ta gudanar ya nuna cewa, tun a ranar 2 ga watan Agustan shekarar 2019 ne jami’an ‘yan sandan Kamaru suka kama dan Jarida Ajiekah Abwue da aka fi sani da Samuel Wazizi, bayan kwana biyar kuma suka mika shi ga jami’an sojin Kasar, kuma tun wancan lokaci babu wanda ya sake jin duriyarsa. Har sai ranar 5 ga watan Yunin shekarar 2020 dinnan da muke ciki, ma'aikatar tsaron kasar cikin wata sanarwa da ce dan jaridar ya mutu watanni goma da suka gaba.

A cikin sanarwar ta soji, ta ce Wazizi da suke zargi da taimakawa 'yan aware masu dauke da makamai, ya mutu ne sakamakon rashin lafiya, ba wai azabtarwa ba, kuma tun awancan lokaci suka sanar da 'yan uwansa mutuwar.

To saidai ‘yan uwansa sun musanta hakan, inda suka ce tsabar gallaza mishi azaba ne ya yi sanadin ajalinsa, kuma babu wanda ya tuntube su dangane da halin da yake ciki tun bayan tsare shi.

Yanzu haka kungiyoyin 'yan jaridu na ciki da wajen kasar na neman ganin an gudanar da bincike tare da hukunta wadanda suka kashe dan jaridar, ko a ranar Talata saida kungiyar 'yan jaridun kasar ta gudanar da zanga-zangar bukatan haka, tare da neman sallamar daukacin 'yan jaridun da kasar ke tsare da su a gidajen kaso.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.