Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Mataimakin shugaban Sudan ta Kudu ya harbu da coronavirus

Mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudu Riek Machar ya harbu da kwayar cutar coronavirus kamar dai yadda ofishinsa ya sanar.

Mataimakin shugaban Sudan ta Kudu Riek Machar.
Mataimakin shugaban Sudan ta Kudu Riek Machar. REUTERS/Stringer
Talla

Bayan tabbatar da cewa Machar ya kamu da cutar, daga bisani an yiwa matarsa da ke matsayin ministar tsaro Angelina Teny da kuma wani ma’aikaci a ofishinsa gwaji, sakamakon kuma ya nuna suma sun harbu da cutar.

Sudan ta Kudu da har yanzu bata gama murmurewa daga yakin basasar shekaru 6 ba, alkalumman hukumomin lafiya sun tabbatar da cewar mutane 339 ne suka kamu da coronavirus a kasar, 6 daga cikinsu kuma sun mutu.

Tuni jami’an lafiay suka bayyana damuwa kan halin da kasar ta Sudan ta Kudu ke ciki, dangane da yaki da cutar coronavirus, la’akari da cewar har yanzu mutane dubu da 908 kawai aka yiwa gwajin cutar, al’ummar kasar da yawanta ya kai miliyan 10 da dubu 980.

A makon jiya gwamnatin kasar ta sanar da cewa, annobar ta coronavirus ta bulla cikin wani sansanin akalla mutane dubu 30 da rikici ya raba da muhallansu a Juba, babban birnin kasar, inda gwaji ya tabbatar da kamuwar ‘yan gudun hijira 2.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.