Isa ga babban shafi

Kanjamau ka iya halaka karin 'yan Afrika dubu 500 saboda coronavirus

Majalisar Dinkin Duniya tayi gargadin cewa, mace-macen masu da nasaba da cutar Kanjamau, ka iya rubanyawa a yankin kasashen Afrika da ke Kudu da Sahara, muddin masu fama da cutar suka gaza samun kulawa a wannan lokaci da hankula suka karkata kan yaki da annobar coronavirus.

Likita yayin yiwa wata mata gwajin cutar HIV a Kampala, babban birnin kasar Uganda.
Likita yayin yiwa wata mata gwajin cutar HIV a Kampala, babban birnin kasar Uganda. REUTERS/Euan Denholm
Talla

Katse bada tallafin magani ga masu dauke da HIV na tsawon watanni shida saboda coronavirus, ka iya haddasa asarar rayukan karin mutane sama da dubu 500 daga bana zuwa badi a yankin kasashen Afrika da ke kudu da Sahara, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya da Hukumar Yaki da Kanjamau ta Majalisar Dinkin Duniya suka yi gargadi a cikin wata sanarwar hadin-guiwa.

Hukumomin biyu sun ce, katse bada kulawar ka iya maida hannun agogo baya, kamar yadda aka gani a shekarar 2008, lokacin da mutane sama da dubu 950 suka mutu saboda Kanjamau a yankin na Kudu da Saharar Afrika.

Kazalika a shekarar 2018, kimanin mutane dubu 470 sun mutu a yankin bisa fama da rashin lafiyar da ke da alaka da cutar ta Kanjamau.

Har ila yau, hukumomin biyu na Lafiya, sun ce, rashin bai wa masu cutar kulawa a wannan lokaci, zai rusa nasarar da aka samu ta hana yaduwar cutar daga uwa zuwa ga danta.

A cewar wakilan hukumomin, kasashe irinsu Mozambique da Malawi da Zimbabwe da Uganda, ka iya fuskantar karuwar matsalar yaduwar Kanjamau tsakanin kananan yara saboda katse kulawar da aka saba bai wa iyaye mata da ke fama da cutar.

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya, Tedros Adhanom Gbebreyesus, ya ce, tuni wasu kasashe suka fara aiwatar da wasu matakai don ganin cewa, masu fama da HIVn sun karbi tarin kunshin magunguna da kuma kayayyakin gwaje-gwajen jinya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.