Isa ga babban shafi
Sudan

Shekara daya cur da kawar da Al-Bashir daga shugabancin Sudan

A kwana a tashi yau shekara daya kenan cur da kawar da Umar Hassan al-Bashir daga karagar mulkin kasar Sudan bayan share tsawon kwanaki ana zanga-zangar nuna kin jinin gwamnatinsa.

Hambararren shugaba Omar el-Béchir cikim, kejin kotun birnin Khartum 31 agustan 2019. REUTERS/Mohamed Nureldin Abdallah
Hambararren shugaba Omar el-Béchir cikim, kejin kotun birnin Khartum 31 agustan 2019. REUTERS/Mohamed Nureldin Abdallah Reuters
Talla

Al-bashir, wanda ya mulki kasar Sudan tsawon shekaru 30, mataimakinsa ne janar Awad Ibn Aouf ya sanar da cewa ya sauka daga karagar mulki bayan tarzomar da ta samo asali sakamakon kara farashin biredi a kasar.

Har zuwa lokacin saukarsa daga karaga, hambararren shugaba Umar al-Bashir ya kasance mai samun cikakkiyar kariya daga hukumar leken asirin kasar karkashin jagorancin Salah Gosh da kuma wata runduna ta musamman da ke karkashin jagorancin janar Mohamed Hamdan Dagalo.

Yanzu haka dai tsohon shugaban na tsare ne a gidan yari, yayin da kotun duniya da ke Hague ke kokarin ganin an mika ma ta shi domin ya fuskanci shari’a bisa zargin aikata laifufukan yaki a yankin Darfur.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.