Isa ga babban shafi

Ghana tayi bikin cika shekaru 53 da samun ‘yancin kai

An gudanar da bukukuwan cika shekaru 63 da samun ‘yancin cin gashin kai daga Turawan mulkin mallaka a kasar Ghana.

Wani dan kasar Ghana rike da Tutar kasar
Wani dan kasar Ghana rike da Tutar kasar Elcio Ramalho/RFI
Talla

Bikin na bana, kamar yadda aka saba, ya hada da faretin jami’an tsaro da ‘yan makaranta da kuma jawabi daga shugabanni a dandalin ‘yanci dake kasar.

Shugaban kasa Nana Addo Dankwa Akufo-Addo yace manufar su a Ghana itace aiki tukuru wajen ciyar da kasar gaba, wanzar da zaman lafiya da kuma walwalar jama’a.

Akufo-Addo yace nauyin da suka dauka a matsayin kasar Afirka ta farko dake yammacin sahara wajen samun ‘yanci ba wai na gina kasar da ta cigaba kawai har ma da tabbatar da duniya da bakaken fata cewar zasu iya tafiyar da mulki yadda ya dace da samar da cigaba da kuma farantawa al’ummar su rai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.