Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Za a kafa gwamnatin hadin gwiwa mai garwaye da 'yan tawaye a Sudan ta Kudu

Shugaban Sudan ta Kudu Sal Va Kirr da jagoran yan tawayen Kasar Riek Machar sun amince da hada gwamnatin hadin gwiwa bayan shafe tsawon shekaru 6 ana gwabza yakin da yaki ci yaki cinyewa a Kasar.

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir
Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir REUTERS/Mohamed Nureldin Abdallah/File Photo
Talla

Bayan zaman tattaunawar sulhu tsakanin jagororin bangarorin biyu a birnin Juba, Machar ya bayyana ranar 22 ga watan Fabarairun nan da muke ciki a matsayin ranar kafa sabuwar gwamnatin hadin gwiwa na kasar kamar yadda suka yarje, yayin da ya ce suna kan tattauna sauran batutuwan da a baya suka haifar da cikas ga shirin, dan kawo maslaha.

Shi kuwa shugaba Sal Va Kirr ya ce wannan ne karo na 3 da ake amincewa da gwamnatin hadaka a sudan ta kudu tun bayan da kasar ta samun yancin kai a shekarar 2011.

Dadadden yakin da bangarorin biyu suka yi ta gwabzawa ya yi sanadiyar kashe mutane dubu 380 ya kuma tilasta wa wasu mutane miliyan 4 ficewa daga gidajensu.

Shugaba Kirr ya bayyana yi wa gwamnatinsa garambawul yayin da yace daga juma’an nan zai soma da zaben Riek Machar a matsayin mataimakinsa, kana a ranar 22 ga watan fabarairun nan da muke ciki zai sake sabon gwamnati.

Shugaban ya kuma ce zai dauki nauyin tabbatar da tsaron Machar da ma yankin Juba baki daya, wanda dakarun hadakan kasar dake karbar horo a halin yanzu zasu gudanar. Kana Yayi kira ga yan gudun hijirar kasarsa kimanin dubu 190 wadanda ke karkashin kulawar majalisar dinkin duniya su koma gida saboda nasarar samun zaman lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.