Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

An yiwa baki ma'aikata 9 kisan gilla a Afrika ta Kudu

Rahotanni daga Afrika ta kudu sun ce gungun 'yan kasar ma’aikatan wani kamfanin hakar ma'adanai sun yiwa takwarorinsu baki daga Lesotho kisan gilla ta hanyar jefe su da duwatsu har lahira, a yammacin birnin Johannesburg.

An yiwa bakin-haure masu hakar ma'adanai kisan gilla a Afrikia ta Kudu.
An yiwa bakin-haure masu hakar ma'adanai kisan gilla a Afrikia ta Kudu. Africanews
Talla

Yanzu haka dai jami’an tsaro sun kaddamar dafarautar gungun mutanen da suka tafka danyen aikin, kamar yadda rundunar ‘yansandan kasar ta Afrika ta kudu ta tabbatar a yau asabar.

Wata kididdiga da hukumar kare hakkin dan adam ta kasar ta fitar a baya bayan nan ta nuna cewar, Afrika ta kudu na tsakanin kasashen dake kan gaba wajen hadari ga baki ‘yan kasashen waje, inda a tsakanin watan Afrilu na 2018 zuwa Maris na shekarar bara, ‘yan asalin kasar suka halaka baki dubu 21,000, kwatankwacin kashe baki 58 a kowace rana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.