Isa ga babban shafi
Afrika ta Tsakiya

Rayukan mutane 50 sun salwanta a sabon rikicin kabilanci

Kimanin mutane 50 sun rasa rayukansu a gabashin Jamhuriyar Afrika ta tsakiya, yayin fadan da aka gwabza tsakanin wasu kungiyoyin mayakan sa kai a Bria, birni mafi girma a yankin mai arzikin lu’u lu’u.

Wasu motocin sulken dakarun wanzar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya.
Wasu motocin sulken dakarun wanzar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya. AFP/FLORENT VERGNES
Talla

Yayin karin bayani kan halin da ake ciki, mai Magana da yawun gwamnati Evariste Binguinidji, ya bayyana fargabar cewa adadin wadanda suka mutu a rikicin ka iya zarta 50, la’akari da cewa iyalai da dama sun gaggauta binne ‘yan uwansu bayanda kura ta lafa.

Rikicin mai alaka da kabilanci ya barke tsakanin gungun mayakan sa kan ne a karshen makon jiya, kwanaki kalilan bayan janyewar dakarun wanzar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya daga birnin na Bria mai arzikin lu’u lu’u, kuma a dai dai lokacin da mazauna yankin da suka tsere a baya ke komawa gida.

A shekarar 2013 kazamin rikici mai alaka da kabilanci da addini ya barke a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya, abinda ya haifar da kafuwar kungiyoyin mayaka na sa kai, wadanda ke gwabza fada da juna kan dimbin arzikin ma’adanan karkashin kasa.

Yanzu haka dai fiye da kashi 2 bisa 3 na fadin Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya na karkashin ikon kungiyoyin mayakan sa kai, zalika fiye da kashi 1 bisa 4 na al’ummar kasar sun tsere daga muhallansu, dalilin tashin hankalin da ya soma a 2013.

A farkon shekarar 2019 wakilan Gwamnatin kasar tare da wakilan kungiyoyin 'yan Tawaye 14 sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya.

Kungiyoyi mayakan sa kai da suka amince da sulhun kuwa 14 ne, da ke rike da yankuna daban daban da ya kai kashi 80 na fadin kasar, tun bayan tashin hankalin da ya biyo bayan juyin mulkin da aka yi wa shugaba Francois Bozize a shekarar 2013, da ya jefa kasar cikin yaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.