Matakan kare kai daga kamuwa da cutar Coronavirus a Afrika
Bayan bulluwar cutar Coronavirus a China da wasu kasashe da suka hada da Amurka,Faransa,Austria. A Nahiyar Afrika wasu kasashe sun soma daukar matakan kare kai a tashoshin sauka dama tashin jiragen saman kasashen su.
Wallafawa ranar:
Wasu daga cikin kasashen da yanzu haka ake samu yawaitar saukar yan China da kuma suka soma daukar matakai sun hada da Najeriya,Nijar, Kenya, Habasha, Afrika ta kudu, Ghana, Sanegal.
Kamar dai yada hukumar lafiya ta Duniya WHO ta yi gargadi, wadanan kasashe sun samar da wurare na kebe duk wani mutum ko matafi dake fama da zazzabi.
Cutar da yanzu ta hadasa mutuwar mutane sama da 50 a China yayinda wasu kusan dubu biyu ke kwance a asibiti.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu