Isa ga babban shafi

Wani dan jarida na cikin matsanaicin hali a kurkukun Chadi - RSF

Kungiyar dake kare hakkin ‘yan jaridu ta Duniya RSF ta nuna damuwa kan matsanaicin halin da wani dan jaridar kasar Chadi ke rayuwa a gidan kaso, inda ta bukaci gwamnatin kasar da ta gaggauta sakin sa.

Editan jaridar Salam Info a kasar Chadi, Martin Inoua Doulguet, a gidan kason da yake tsare a birnin N'Djamena na kasar Chadi
Editan jaridar Salam Info a kasar Chadi, Martin Inoua Doulguet, a gidan kason da yake tsare a birnin N'Djamena na kasar Chadi RSF
Talla

Acewar RSF, Watanni uku bayan an yanke masa hukuncin shekaru uku a kurkuku, Martin Inoua Doulguet, editan jaridar Salam Info a kasar ta Chadi, na cikin halin kunci a wani gidan kaso dake kasar, yana kwanciya a kar, kana sai ya biya kudi kafin samun tsaftacencen bahaya.

A ranar 16 ga watan Agustan wannan shekara ta 2019 aka kame dan jaridar aka kuma yanke masa hukuncin daurin shekaru 3 a gidan kaso a watan Satumba, bisa laifin kage, da hada baki don bata suna.

Tsohon ministan lafiyar kasar Chadi ya shigar da kara, bayan da jaridar Salam Info ta zarge shi da lalata da ‘yar dan uwansa.

Lauyan dan jaridan Maitre Olivier Gouara yace, abokin nasa na rayuwa cikin matsanaicin hali, domin kuwa bai samun damar zuwa asibitin kula da lafiya dake gidan kason, kana dan mintu ake baiwa duk wanda ya ziyar ce shi.

A cewar kungiyar RSF, lauyanta dan kasar Faransa da ya ziyarci gidan kason da dan jaridar ke tsare, ya tabbatar da halin da yake ciki, inda yace dan jaridan na fama da tsangwama daga abokan zaman sa, wadanda suka yi masa duka tun ranar farko da ya isa gidan.

Shugaban kungiyar da ke kula da Afirka Arnaud Froger, yace matakin gwamnatin Chadi na tsare dan jaridan tauya ‘yancin fadin albarkacin baki ne, idan akayi la’akari da labarin da ya wallafa dangane da ministan lafiyar, inda ya bukaci hukumomin kasar da suyi gaggawar sallamar dan jaridar.

Kasar Chadi ce ta 122 a kasashe 180 a kiyasin Kungiyar RSF na 2019 a kare hakkin ‘yan jaridu ta Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.