Isa ga babban shafi
Afrika

Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 265

Akalla mutane 265 sun rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa a wasu kasashen gabashin Afrika, inda aka kwashe tsawon watanni biyu ana tafka ruwan sama babu kakkautawa, yayin da ruwa ya shanye gonaki da gidajen karkara.

Mutane da dama sun rasa muhallansu saboda ambaliyar ruwa a kasashen gabashin Afrika
Mutane da dama sun rasa muhallansu saboda ambaliyar ruwa a kasashen gabashin Afrika Photo: Adrien Barbier
Talla

Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP ne ya tattara wadannan alkaluman mamatan, yayin da masana yanayi suka gargadi cewa, nan gaba za a samu makamancin wannan ibtila’in.

Ruwan saman da aka tafka kamar da bakin-kwarya ya shafi mutane kusan miliyan 2, inda kuma ya yi awon gaba da dubban dabbobi a kasashen Kenya da Somalia da Burundi da Tanzania da Sudan ta Kudu da Uganda da Djibouti da kuma Habasha.

Yanzu haka ana dari-darin yaduwar cutukan da ake dauka ta hanyar ta’amulli da gurbataccen ruwan sha da kuma tsunduma cikin ibtila’in yunwa saboda ruwan saman da zai sauka nan da ’yan makwanni a yankin na gabashin Afrika.

A Burundi, mutane 38 suka gamu da ajalinsu cikin dare a ranar Laraba biyo bayan saukar ruwan sama mai karfi, lamarin da ya haddasa zaftarewar kasa a yankin arewa maso yammacin kasar.

A can Kenya kuwa, mutane 132 suka mutu, sannan dubu 17 suka rasa matsugunai, inda kuma ambaliyar ruwan ta mamaye makarantu da hanyoyi da cibiyoyin kiwon lafiya, sai kuma Tanzania, inda mutane 55 suka riga mu gidan gaskiya.

A Uganda mutane 8 suka mutu, sai kuma 22 da suka mutu a Habasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.