Kotu na tuhumar tsohon ministan Jammeh bisa laifin kisa
Hukumomin kasar Gambia sun gurfanar da tsohon ministan gwamnatin Yahya Jammeh, Yankuba Touray a gaban kotu, saboda kin amsa tambayoyi a gaban Hukumar kasar ta Tantance Gaskiya da Sasanta Jama’a.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Touray wanda ke cikin tawagar tsohon shugaban da tayi juyin mulki a shekarar 1994, ya ce yana da kariyar da ta hana shi bada ba’asi a gaban hukumar.
Hukumar ta Tantance Gaskiya da Sasanta Jama’a na tuhumar tsohon ministan ne da hannu wajen kashe ministan kudin kasar ta Gambia a watan Yuni na shekarar 1995, da kuma sojoji a watan Nuwambar shekarar 1994.
Lauyan Touray Abdoulie Sissoho, ya bukaci bada belinsa da kuma cigaba da shari’ar a cikin wannan makon.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu