Isa ga babban shafi
Najeriya-Amnesty

Amnesty ta zargi jami'an tsaron Najeriya da gallazawa Jama'a

Kungiyar kare hakkin Bil Adama ta Amnesty International a Najeriya ta yi zargin cewar har yanzu jami’an tsaron kasar na gallazawa jama’a da kuma cin zarafin su ta hanyoyi daban daban.

Tambarin kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International
Tambarin kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International @សហការី
Talla

Wata sanarwa da kungiyar ta fitar ya bayyana cewar da dama daga cikin irin wadannan mutane da aka ci zarafin su ba sa samun taimakon da ya dace ko da sun kai kara a wajen shugabannin jami’an tsaron da kuma kotuna.

Daraktan kungiyar a Najeriya, Osai Ojigho ta ce duk da dokar kasar na haramta azabtar da mutane da kuma kafa kwamitin sake fasalin rundunar SARS, har yanzu ana samun matsalar.

Kungiyar ta Amnesty International dai ta jima ta na diga ayar tambaya kan gallazaw da jami'an tsaron Najeriya galibi sojoji da kuma sashen manyan laifuka na rundunar 'yan sanda wato SARS ke yiwa jama'ar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.