Isa ga babban shafi
Afrika-Najeriya

An bude taron yaki da cin hanci da rashawa na kasashen Afrika

Yau talata shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jagoranci bude taron yaki da cin hanci da rashawa na kasashen Afirka.

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari. Reuters
Talla

Taron ya mayar da hankali ne kan yadda za’a dakile amfani da kudaden sata wajen tafiyar da harkokin siyasa da kuma zabe.

Shugabannin kasashen Afirka da suka halarci taron sun hada da shugaba Buhari na Najeriya, da Paul Kagame na Rawanda da takwarorinsu na Ghana da Liberia da Senegal.

Daga cikin wadanda za su gabatar da jawabi yayin taron akwai shugaban kasar Rwanda Paul Kagame, wanda zai yi magana kan sahihin zabe, matsalar baiwa masu kada kuri’a cin hanci da kuma yadda za’a magance matsalar ta cin hanci da ta fadada a tsakanin al’umma.

Tsohon shugaban hukumar zaben Najeriya Farfesa Attahiru Jega kuwa, jawabinsa ya mayarda da hankali ne kan rage barnatar da kudade kan gudanar da zabe, da kuma amfani da kudi kan masu kada kuri’a, sai kuma nauyin da ya rataya a wuyan hukumomin tsaro, wajen tabbatar da doka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.