Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

Boko Haram ta yi garkuwa da wasu mutane 50 a Gamboru

Wasu bayanai sun ce ‘yan Boko Haram sun sace mutane akalla 50 da lokacin da suka shiga daji domin neman itace a kusa da garin Gambaru wanda ba ya da nisa da iyakar Najeriya da Kamaru.

Akwai dai rahotanni da ke cewa mutane 2 daga cikin wadanda boko haram din ta sace sun samu gudowa tare da sanar da hukumomi.
Akwai dai rahotanni da ke cewa mutane 2 daga cikin wadanda boko haram din ta sace sun samu gudowa tare da sanar da hukumomi. REUTERS/Emmanuel Braun
Talla

Shaidu sun ce mutanen da aka sacen dukkaninsu ‘yan gudun hijira ne da ke zaune a wani sansanin ‘yan gudun hijira a kauyen Bulakesa, kuma a cewar jagoran jami’an tsaron sa-kai a yankin Umar Kachalla, mai yiyuwa ne adadin wadanda sacen ya fi 50.

Akwai dai rahotanni da ke cewa mutane 2 daga cikin wadanda boko haram din ta sace sun samu gudowa tare da sanar da hukumomi.

Kawo yanzu dai babu labarin halin da mutanen 50 su ke ciki yayinda wani mazauni garin Babagana Musa ke cewa tabbas suna cikin fargabar me zai je ya zo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.