Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamna Lalong na Plateau ya ce kisan Janar Alkali shiryayyen abu ne

Gwamnan Jihar Plateau da ke Najeriya, Simon Lalong ya kai ziyarar ta’aziya ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da shugaban rundunar sojin kasar Janar Tukur Buratai da kuma iyalan Janar Idris Alkali da aka yi wa kisan gilla a Jiharsa.

A cewar Lalong babu shakka an jima ana shirya kisan babban jami'in amma babu shakka za su yi dukkan mai yiwuwa wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar ta Plateau da kewaye.
A cewar Lalong babu shakka an jima ana shirya kisan babban jami'in amma babu shakka za su yi dukkan mai yiwuwa wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar ta Plateau da kewaye. RFI hausa
Talla

Lalong ya bayyana cewar kashe tsohon hafsan Janar Alkali wata manakisa ce da aka kitsa da dadewa, inda yace za su cigaba da daukan matakai daban daban wadanda za su tabbatar da zaman lafiya a Jihar baki daya.

Kuna iya sauraron hirar da RFI Hausa ta yi da Gwamnan a shirinmu na karfe 7 gobe da safe.

Idan ba a manta ba, an gano gawar Marigayi Janar Alkali ne ranar Laraba cikin wata tsohuwar rijiya ta Guchwet da ke yankin Shen a karamar hukumar Jos ta kudu bayan fara nemansa tun a ranar 3 ga watan Satumban da ya gabata lokacin da ya bace a kan hanyarsa ta zuwa Bauchi daga Abuja.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.