Isa ga babban shafi
Guinea Conakry

Alpha Conde yayi kakkausar suka kan manufofin Faransa

‘Baya ga samun yancin kai, manufofin Faransa ga kasar Guinee sun kasance marasa kyau, tsawon lokaci alakarmu ta kasance mai tsami sosai, sai bayan share tsawon shekaru ne aka samu daidaito ,Shugaban kasar Alpha Conde a wata ganawa da manema labarai ya sanar da haka.

Alpha Condé.Shugaban kasar Guinee Conakry
Alpha Condé.Shugaban kasar Guinee Conakry Reuters / Ludovic Marin
Talla

Shugaban Guinee Conakry Alpha Conde, ya ce alhaki ya rataya a wuyan kasar Faransa dangane da wasu matsalolin da kasar ta fuskanta da ma wadanda take fama da su a halin yanzu.

Bayan mun kada kuri’ar samun ‘yancin kai, Faransa ta sanya wa Guinee kangi iri-iri, dole sai da muka nemi tallafi daga Tarayyar Soviet da kuma China.

Faransa ta janye dukkanin kwararrin ma’aikatanta daga kasarmu, alhali ta sani cewa ba mu da kwarewa a lokacin, wadannan abubuwa ne da ya kamata matasan kasar Guinee da ma takwarorinsu na Afirka su sani, musamman a wannan lokaci na tunawa da ‘yancin kan da muka sama a shekarar 1958.

Shugaba Alpha Conde ya bayyana rashin jin dadin sa ganin rawar da Faransa ta taka a lokacin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.