Isa ga babban shafi
Congo Dimokuradiyya

Moise Katumbi 'zan koma gida Congo'

Wani na hannun daman daya daga cikin shugabannin yan adawan Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo, Moise Katumbi, yace ya tattauna da wakilan Majalisar Dinkin Duniya kan shirin komawa gidan mai gidan sa domin shiga takarar zaben shugaban kasar da za’ayi nan gaba.

Moise Katumbi, daya daga cikin masu adawa da Shugaba Joseph Kabila a Congo
Moise Katumbi, daya daga cikin masu adawa da Shugaba Joseph Kabila a Congo Getty Images
Talla

Yau ake saran Katumbi, wanda tsohon Gwamnan yankin Katanga ne ya koma gida domin shiga takarar zaben bayan gudun hijirar da ya yi a kasar Belgium tun watan Mayun shekarar 2016.

Rahotanni na cewa ana shirin kama Katumbi da zaran ya sauka a kasar saboda samun sa da laifin hayan sojan gona da kuma mallakar fasfo din kasar Italia.

Mai Magana da yawun dakarun majalisar dinkin duniya a kasar, Florence Marchal tace ba aikin su bane samar da tsaro ga daidaikun mutane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.