Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Robert Mugabe ya yi kiran kada tsohuwar jam'iyarsa ta ZANU PF a zaben gobe litanin

Yau a gobe litanin ne ake gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki a Zimbabwe, karo na farko tun bayan kifar da gwamnatin Robert Mugabe wanda ya jagoranci kasar tsawon shekaru 37.

Tsohon shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe, a lokacin taron manema labarai a  Harare, 29 yuli 2018,
Tsohon shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe, a lokacin taron manema labarai a Harare, 29 yuli 2018, REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

‘Yan takara biyu ne ke shirin fafatawa da juna a zaben na yau, wato Emmerson Mnagagwa mai shekaru 75 a duniya wanda kuma ya kwace mulki daga hannun Robert Mugabe, da kuma Nelson Chamisa matashin dan siyasa mai shekaru 40 a duniya.

Kafin wannan zabe dai, hasashe ya yi nuni da cewa idan har ma dan takarar jam’iyya mai mulki zai yi nasara a zaben, to ba za a samu wata tazara mai yawa a tsakaninsu ba, yayin da wasu ke hasashen cewa, za a iya zuwa zagaye na biyu a ranar 8 ga watan gobe kafin fitar da gwani a tsakaninsu.

A Jajibirin wannan zabe dai tsohon shugaban kasar Robert Mugabe, ya ce ba zai jefa wa dan takarar jam’iyyarsa ta ZANU-PF wato Emmerson Mnangagwa kuri’arsa ba, inda ya yi kira ga sauran al’ummar kasar da su kada kuri’ar kayar da gwamnatinsa.

Mugabe ya ce, ba zai jefa kuri’arsa ga wadanda suka cutar da shi ba, tare da bayyana shugabancin Mnangagwa a matsayin wanda ba ya da halasci, abin da ke nufin cewa, zai mara wa dan takarar jam’iyyar adawa ta MDC Nelson Chamisa baya a zaben na ranar litanin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.