Isa ga babban shafi
Burkina Faso

Burkina Faso ta samu ci gaba a fanin kiwon lafiya

Hukumomin Burkina Faso sun samu gagarumar nasarar ceto rayukan kananan yara kusan 3,000 sakamakon fadakarwar da suke yi dangane da kula da lafiyar jama’a ta kafofin rediyo a kasar.

Bada kulawa zuwa yaran da suka kamu da cutar Malaria a Afrika
Bada kulawa zuwa yaran da suka kamu da cutar Malaria a Afrika RFI/Caroline Paré
Talla

Sakamakoon binciken da masana suka gudanar wanda aka wallafa a mujallar kula da lafiyar Birtaniya da ake kira ‘Global Health’ yau talata, yace fadakarwar da masana kiwon lafiya suka yi tayi ta kafar rediyo a yankunan karkara dangane da cututtukan zazzabin cizon sauro da nimoniya da kuma gudawa ya taimaka wajen ceto rayukan yara kanana dake kasa da shekaru 5 har kusan 3,000 a Burkina Faso.

Shugaban jami’an da suka gudanar da binciken, Roy Head yace, sakamakon binciken nasu ya nuna cewar amfani da kafofin yada larabai wajen janyo hankalin jama’a domin kula da lafiyar su na da matukar tasiri.

Jami’in yace gidajen rediyo 7 akayi amfani da su wajen fadakar da jama’a dangane da illolin wadannan cututtuka da kuma inda ya kamata su samu magani.

Farfesa Simon Cousens, daya daga cikin wadanda suka jagoranci binciken ya bayyana cututtukan zazzabin cizon sauro da nimoniya da gudawa na daga cikin cututtukan da suka fi kashe kanana yara a yankin Afirka dake kudu da Sahara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.