YAU ake saran shugaban Faransa Emmanuel Macron zai fara ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Najeriya wadad zata kai shi Abuja inda zai gana da shugaba Muhamamdu Buhari kafin zarcewa Lagos domin gudanar da wasu ayyuka.Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Khalifa Dikwa kan ziyarar kuma ga yadda hirar su ta gudana.
Sauran kashi-kashi
-
Hon Sama'ila Muhammad a kan dokar kare hakkin Yara a Najeriya
'Yan Najeriya na ci gaba da tafka mahawara a kan dakatar da auran wasu marayu 100 da ministar kula da harkokin matan kasar ta bukata a Jihar Neja, saboda abinda ta kira sabawa dokar kare hakkokin yara.Yanzu haka kungiyoyi daban daban sun ruga kotu domin kalubalantar ministar.Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da lauya kuma tsohon 'dan majalisar tarayya, Hon Samaila Muhammed, wanda yace dokar da ake magana a kai ta sabawa dokokin kasa.Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraren hirar.20/05/202403:34 -
Attahiru Bafarawa kan shirin ƴan adawa na tinkarar jam'iyya mai mulki a 2027
A Najeriya, yanzu haka wasu daga cikin manyan ‘yan adawar ƙasar cikin su harda wadanda suka tsaya takarar zaɓen shekarar 2023 sun fara tintibar juna domin tsara yadda za su tinkari jam’iyya mai mulki a zaɓe mai zuwa. Rahotanni sun ce akwai yiwuwar kafa wata sabuwar jam’iyya domin kalubalantar gwamnati mai ci.Dangane da wannan yunkuri, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da tsohon Gwamnan Jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa. Kuna iya latsa alamar sauto domin sauraren hirar.15/05/202403:18 -
Farfesa Kailani Muhammed a kan batun satar danyen mai a Najeriya
Hukumomin Najeriya sun ce sun kama jiragen ruwa 14 da ake satar danyan man fetur a Neja Delta tsakanin watan Janairun wannan shekara zuwa karshen watan Maris.Rundunar dake aikin samar da tsaro a Jihar Rivers tace wannan bai hada da kananan jirage 90 da kuma mutane 74 da ta kama ba, wadanda ke yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa.Dangane da wannan matsala, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Kelaini Muhammed, masani a kan harkar gas da man fetur, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.14/05/202403:31 -
Kwamandan MNJTF Janar Ibrahim Sallau kan nasarar su a yankin tafkin Chadi
Rundunar hadin gwuiwa da ke yaƙi da mayakan Boko Haram a Tafkin Chadi da ake kira MNJTF ta sanar da kashe mayaka 299 a cikin watanni 10 da suka gabata da kuma samun wasu 273 da suka mika kansu cikin lumana. Kwamandan rundunar Manjo Janar Ibrahim Sallau Ali ya bayyana haka ga Babban Editan sashin Hausa Bashir Ibrahim Idris a tattaunawar da suka yi ta wayar tarho bayan ya kwashe watanni 10 yana jagorancin rundunar mai cibiya a kasar Chadi.Ku latsa alamar sauti domin sauraren zantawar su.09/05/202406:33 -
Farfesa Dicko Abdurrahmae kan zaben Chadi
Yau Litinin aka bude rumfunan zabe a kasar Chadi, don zaben shugaban kasa da zai kafa sabuwar gwamnatin Chadi da ta kasance karkashin mulkin soji na tsahon shekaru 3.06/05/202403:30