Isa ga babban shafi
Wasanni-Najeriya

Rohr zai ajje aikin horar da Super Eagles

Wasu rahotanni na nuni da cewa kociyan kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Gernot Rohr na gab da ajje aikinsa inda zai koma horar da kungiyar kwallon kafar Aljeriya.

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Gernot Rohr.
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Gernot Rohr. REUTERS/Louafi Larbi
Talla

Algeria dai a baya-bayan nan ne ta kori mai horar da ‘yan kwallon na ta Rabah Madjer bayan rashin tabuka abin kirkin da tawagar kasar ta yi a wasannin sada zumuncin da ya gudana tsakaninta da Iran, Saudi Arabia da Cape Verde da kuma Portugal.

Gernot Rohr wanda ya tsawaita kwantiraginsa da Najeriya zuwa 2020 gabanin tafiya gasar cin kofin duniya, ya ce babu tabbacin dorewar aikinsa bayan rashin nasarar Super Eagles a Rasha.

Kociyan wanda ya dade yana aikin horar da kasashen Afrika irinsu Nijar Birkinafaso da kuma Gabon zai iya tafiyar da tawagar ta Algeria la’akari da cewa ya horar da kungiyoyi kamar su Bordeaux OGC da Nice da kuma Nantes na Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.