Isa ga babban shafi
Afrika

An bude taron kasashen Afrika na AU

A yau Lahadi aka soma taron kwanaki biyu na shugabannin kasashen Afrika a Nouakchott, babban birnin kasar Mauritania.

Shugabannin kasashen Nijar,Chadi da Najeriya a taron kasashen Afrika a Mauritania
Shugabannin kasashen Nijar,Chadi da Najeriya a taron kasashen Afrika a Mauritania Sunday Agazi
Talla

Taron zai mayar da hankali kan manyan batutuwan da suka hada da, yaki da cin hanci da rashawa, kawo karshen matsalolin tsaro na rikicin kabilanci da ta’addanci.

Shugabanin zasu kuma tattauna kan inganta huldar kasuwanci da kuma samar da alakar cinikin bai daya.

Wakilan kungiyar kasashen Afrikan AU, zasu tattauna kan warware rikicin Sudan ta Kudu, da kuma maido da kyakkyawar dangantaka tsakanin Habasha da Eritrea, wadanda tuni gwamnatocin kasashen biyu suka soma yunkurin hakan.

Shugaban hukumar gudanarwar kungiyar kasashen Afrika AU, Moussa Faki Mahamat, ya bukaci daukar matakan ladabtarwa, kan wadanda ke karya yarjeniyoyin zaman lafiya tsakanin gwamnatin Sudan ta Kudun da kuma ‘yan tawayen kasar, wato, shugaba Salva Kiir da madugun 'yan tawaye Riek Machar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.