Isa ga babban shafi
Najeriya

Amurka na Jagorantar taro kan sha'anin tsaro a Najeriya

Manyan hafsoshin sojin kasa daga sassa daban daban na Nahiyar Afrika sun fara wani taro kan sha'anin tsaro yau a Abuja babban birnin Najeriya karkashin jagorancin Amurka. Taron na da nufin hada hannu tsakanin kasashen don yaki da ayyukan ta'addanci.

Wasu dakarun sojin Najeriya kenan yayin atisayen da suke gudanarwa gabanin kai farmaki wata maboyar boko haram a garin Baga na jihar Borno.
Wasu dakarun sojin Najeriya kenan yayin atisayen da suke gudanarwa gabanin kai farmaki wata maboyar boko haram a garin Baga na jihar Borno. REUTERS/Tim Cocks
Talla

Taron manyan hafsoshin sojin kasan na Afrika a cewar Amurka zai taimaka matuka ta yadda kasashen za su hada hannu don kammala fatattakar kalubalen tsaron da ke barazana ga nahiyar.

Hafsoshin sojin kasa daga kasashen Angola Kamaru Masar Kenya da kuma Rwanda za su yi musayar bayanai kan yadda za a shawo kan matsalar tsaron da ta kunshi ayyukan ta'addanci kungiyar Al-shabab a gabashin nahiyar da kuma na kungiyar Boko haram a yammaci.

Gwamnatin Amurka karkashin jagorancin tsohon shugabanta Barrack Obama, kasar ta himmatu wajen yaki da ayyukan ta'addanci a Afrika wanda a lokacin ya fara yaduwa wanda kuma yanzu haka shugaban kasar mai ci Donald Trump ya ce zai dora.

Kafin korarshi daga bakin aiki a watan Maris, sakataren harkokin wajen Amurkan ya gudanar da wata ziyara a kasashen Nahiyar 5 da nufin nuna goyon bayan kasar kan ci gaba da yaki da ayyukan ta'addanci.

Ko a baya-bayan nan ma Amurkan ta jagoranci wani atisayen soji daya kunshi dakaru daga kasashe 26 a jamhuriyar Nijar da nufin fatattakar ayyukan ta'addanci a yankin Sahel.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.