Paul Biya ya bai wa jami'an tsaro umurnin murkushe 'yan aware
Shugaban Kamaru Paul Biya, ya lashi takobin ci gaba da daukar matakin soji don murkushe ‘yan awaren da ke yankin masu amfani da Turancin Ingilishi.
Wallafawa ranar:
Biya ya bayyana aniyarsa ce a yayin jagorantar taron Majalisar Zartaswar kasar na farko da ya jagoranta a jiya Alhamis bayan ya shafe kimanin shekaru biyu ba tare da ya halarci irin wannan taro na mako-mako ba.
A cewar shugaba Biya, daukar matakin soji ne abin da ya fi dacewa da ‘yan awaren matukar ana son dawo da al’amura yadda ya kamata a yankin.
A ranar daya ga watan Oktobam 2017 ne ‘yan awaren suka shelanta kafa kasarsu mai suna Ambazonia, daga kasar Kamaru, yankin da ke da kaso biyar na jama’ar kasar.
Yanzu haka dai shugaba Paul Biya ya bai wa dakarun kasar umarnin kutsawa yankin na ‘yan awaren, cikin shirin yaki, tare da jirage masu saukar ungulu da tankokin yaki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu