Senegal-Turkiyya
Ziyarar Erdogan a wasu kasashen Afirka
A cigaba da ziyarar aiki a wasu kasashen Afirka, a jiya alhamis shugaban Turkiyya Racep Tayyep Erdogan ya isa birnin Dakar na Senegal, inda ya gana da shugaba Macky Sall.
Wallafawa ranar:
Talla
A lokacin wannan ziyara, kasashen biyu sun kulla yarjeniyoyi da dama a fagen tattalin arziki, da suka hada da man fetur, ma’adinai da kuma sufurin jiragen kasa.
A wannan juma’a shugaban na Turkiyya zai isa Bamako kasar Mali, karo na farko a matsayinsa na shugaban kasa. Kafin nan dai Erdogan ya ziyarci kasashen Algeria da kuma Mauritaniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu