Isa ga babban shafi
Afrika

Fiye da mutane dubu 65 ne ke neman mafaka daga Afrika ta tsakiya

Wani rahoton kungiyar bada agajin gaggawa ta Red cross ya nuna cewa akalla mutane dubu bakwai da daru hudu ne rikicin Jamhuriyar afrika ta tsakiya na baya bayan nan ya tilastawa barin gidajensu.

Red Cross ta ce kawo yanzu akwai kimanin mutane dubu 65 da suka nemi mafaka a kauyen Paoua dake da yawan mutane dubu 40.
Red Cross ta ce kawo yanzu akwai kimanin mutane dubu 65 da suka nemi mafaka a kauyen Paoua dake da yawan mutane dubu 40. REUTERS/Carlos Garcia Rawlins
Talla

A cewar Red Cross galibin mutanen na rayuwa ne cikin mawuyacin hali a yankin Markounda.

Fiye da watanni biyu kenan kungiyoyi masu dauke da makamai ke ci gaba da fafatawa da juna kan ikon mallakar yankin, lamarin da ya haddasa mutuwar daruruwan fararen hula.

Red Cross ta ce kawo yanzu akwai kimanin mutane dubu 65 da suka nemi mafaka a kauyen Paoua dake da yawan mutane dubu 40.

Tun cikin shekarar 2013 ne kasar ta Afrika ta tsakiya ta afka cikin rikicin kabilanci dana addini, daya haddasa kisan rashin imani ga jama’a.

Ko a bayan bayan nan majalisar dinkin duniya ta yi gargadi kan yadda yunwa ke ci gaba da hallaka kananan yara a Jamhuriyyar Afrika ta Tsakiyar wadda rikici ya tagayyara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.