Isa ga babban shafi
G5-Sahel

Ayyukan rundunar fada da ta'addanci a yankin Sahel

Matakin farko na fada da ayyukan ta’addanci a yankin Sahel karkashin inuwar rundunar G5-Sahel wanda aka yi wa take da ‘’Hawbi’’ wadda aka kaddamar 27 ga watan oktoban da ya gabata, zai kawo karshe a ranar 11 ga wannan wata na nuwamba.

Tambarin rundunar G5-Sahel
Tambarin rundunar G5-Sahel © RFI/Olivier Fourt
Talla

A tsawon wadannan kwanaki, dakaru 350 daga Mali, 200 daga Burkina Faso da wasu 200 daga Nijar, za su kawo karshen farmaki da samamen da suke gudanarwa tsakanin garin Asongo da ke cikin Mali zuwa Dori a Burkina Faso.

Har ila yau akwai dakaru 180 daga rundunar Barkhane ta Faransa da ke taimaka wa mayakan na G5-Sahel a wannan farmaki, duk da cewa manyan kwamandojinta sun bayyana cewa an dan fuskanci wasu matsaloli.

Wasu daga cikin wadannan matsaloli kuwa sun hada da karancin kayan aiki musamman na sadarwa, da kuma rashin samun hadin-kai daga jama’a.

Wasu daga cikin matsalolin da aka gano a lokacin wannan farmaki, sun hada da rashin fahintar juna a tsakanin kasashen dangane da yadda za a bambanta ‘yan ta’adda, barayi, tsagera ko kuma ‘yan tawaye da ke dauke da makamai a yankin kamar dai yadda babban kwamandan askarawan Burkina Faso Oumarou Sadou ke cewa.

Babban kwamandan askarawan jamhuriyar Nijar kuwa Janar Seyni Garba, cewa ya yi wasu daga cikin farmaki da samamen da suke tsarawa na gaza cimma nasara ne saboda akwai wadanda ga alama ke tsegunta wa ‘yan ta’addar wasu daga cikin matakan da rundunar ke shirin dauka kafin kaddamarwa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.