Gwamnatin Kamaru ta fara tattaunawa da shugabannin yankin Bamenda
Fira Ministan kasar Kamaru, Philemon Yang, ya fara wata ziyarar tuntubar juna a yankin Bamenda, dake arewa maso gabashjin kasar, a kokarin da gwamnatinsu ke yi na na tattaunawa da mutanen yankin, dake amfani da turancin inglishi a yankin, wanda a baya yayi fama da rikice rikicen siyasa da na zamantakewa.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Mista Yang ya gana shuwagabannin kungiyoyin sufuri, malaman makaranta, ‘yan kasuwa, shugabanin kamfanoni, da kuma bankuna a yankin na Bamenda.
Wadanda suka halarci tattaunawar ta jiya Litanin sun gabatarwa Fira Ministan shawarwari kan yadda za’a magance matsalolin yankin, sai dai kuma babu cikakken bayani kan abinda shawarwarin suka kunsa.
Yau Talata ma, gwamnatin kasar ta Kamaru za ta ci gaba da tattaunawar da jagororin yankin na arewa maso yammaci
A baya dai yankin na masu amfani da turancin Ingilishi ya shafe watanni ana zaman dar dar cikinsa sakamakon zazzafar adawa da mutanen yankin ke yi da gwamnatin Paul Biya wadda suka zarga da nuna musu banbanci wajen fifita yankunan da ke amfanin da Faransanci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu