Isa ga babban shafi
Holland

Wani Kamfanin Dutch zai biya diyya ga al'ummar Cote d'ivoire

Tawagar lauyoyin da ke kare dubban al'ummar kasar Ivory Coast wadanda suka cutu sakamakon gubar da wani kamfanin Dutch ya kai kasar a shekarar 2006 sun shigar da kara gaban wata kotu da ke Amsterdam kan bukatar Kamfanin ya biya mutanen diyya.

Ana dai zargin kamfanin na Trafigura da shigar da gubar tashar jiragen ruwa na Abidjan a watan Agustan shekarar 2006.
Ana dai zargin kamfanin na Trafigura da shigar da gubar tashar jiragen ruwa na Abidjan a watan Agustan shekarar 2006. Reuters
Talla

Mau shigar da karar dai na zargin kamfanin da shiga kasar ta Cote d’Ivoire da gubar wato Trafigura, inda guda cikin lauyoyin mutanen Bojan Dekker ke shaidawa kotun a zaman ta na jiya bukatar al'ummar na neman hakkokinsu gabanta.

Yanzu haka dai kotun ta umarci Kamfani da ya biya mutanen da suka cutu su kimanin dubu 107 diyya.

A watan Agustan shekarar 2006 ne dai aka kama tulin tarkacen guba cikin wani jirgin ruwan mai rajistan Panama da suna Probo Koala, da aka ki sauke gubar a tashar ruwan Amsterdam kuma aka karkata akalansa zuwa tashar ruwan Abidjan tare da amfani da ita a yankuna 18 na kasar.

Alkalan Cote d’Ivoire na zargin gubar ta yi sanadin mutuwar mutane 17, inda wasu da dama kuma suka jikkata yayinda kamfani ya yi mirsisi tare da ikirarin ya yi cewa ba shi da masaniya kan gubar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.