Isa ga babban shafi
Najeriya

APC ta ce rashin lafiyar Buhari kalubale ne ga manufofin jam'iyyar

Jam’iyyar APC a Najeriya ta ce rashin lafiya shugaban kasar Muhammadu Buhari lamari ne da ke haddasa tarnaki wajen aiwatar da manyan manufofin gwamnatin da ke kan karagar mulki.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osibanjo a Abuja
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osibanjo a Abuja REUTERS
Talla

Bayan wata ganawa da suka yi da mukaddashin shugaban kasar Yemi Osinbajo a fadarsa da ke Abuja ranar laraba, shugabannin jam’iyyar a matakin jihohi, sun ce sun tattauna ne dangane da lamurran da suka shafi tafiyar kasar.

Henry Ajomale, shugaban jam’iyyar reshen jihar Lagos, ya ce ko shakka babu rashin lafiyar shugaban ya shafi tsari da kuma alkawurran da jam’iyyar ta yi a lokacin yakin neman zabe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.