Isa ga babban shafi
Senegal

Matsalar bara a kasar Senegal

Kungiyoyin kare hakkin Bil Adama sun soki gwamnatin Senegal kan yadda ta kasa daukar matakan magance matsalar barar kanana yara wadanda malaman makarantun allo ke sasu a kasar.

Masu bara
Masu bara Flickr/Philofoto
Talla

A watan Yulin bara gwamnatin ta kaddamar da kamen yaran dake bara cikin su harda yara masu shekaru 4 wadanda suka ce malaman su suke tura su.

Kungiyar Human Rights Watch da Platform for the Promotion and Protection of Human Rights sun ce rashin hukunta malaman dake tura yaran bara ya kasa magance matsalar.

Kungiyoyin sun ce abin takaici ne yadda ake ganin wadanan yara suna yawon bara domin samun abinda zasu ci su kuma kaiwa malaman su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.