Sojoji na ci gaba da bore a Ivory Coast
Ana ta jin harbe-harbe da manyan bindigogi a manyan birane biyu na kasar Ivory Coast inda sojoji ke bore suna neman biyan su albashi mai tsoka da kuma basu gidan kwana don su mallaka.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Majiyoyi na cewa ana ta jin rugugin harsasan ne daga garuruwan Bouake gari na biyu mafi girma a kasar da kuma Korhogo.
Tun Juma'a sojojin suka kama garin Bouake inda suka dasa kansu a wasu muhimman wurare.
Cikin wata sanarwa Ministan Tsaro na kasar Alain-Richard Donwahi ya nemi sojojin da su yi hakuri domin Gwamnati na shirin sauraron koken su.
Boren ya yi sauya zuwa garuruwan Dalao, Daoukro da Odienne.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu