Shirin dandalin siyasa na wannan makon tare da Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya tattauna ne kan rikicin siyasar Gambia, in da shugaba mai ci Yahya Jammeh ya ki amincewa da miki mulki duk da kashin da ya sha a zaben shugabancin kasar da aka gudanar a farkon watan Disamba. Kazalika shirin ya tattauna kan kudirin kasafin kudin shekara mai zuwa da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar wa zaman hadin gwiwa na majalisar tarayyar Najeriya