Isa ga babban shafi
Habasha

Habasha za ta yi sauye-sauye a tsarin zabe

Firaministan Habasha Hailemariam Desalegn ya ce, gwamnati na shirin aiwatar da sauye-sauye a game da tsarin gudanar da zabe na kasar, a wani mataki da ake ganin cewa zai iya kwantar da hankulan ‘yan adawa da ke zanga-zanga. 

Firaministan Habasha Hailemariam Desalegn.
Firaministan Habasha Hailemariam Desalegn. REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

Firaministan ya ce, aiwatar da sauye-sauyen abu ne da zai bai wa illahirin al’ummar kasar samun wakilci musamman a cikin majalisa.

A wannan Talata ne dai shugabar gwamanatin Jamus Angela Merkel ke ziyara a kasar ta Habasha bayan ta ziyarci kasashen Mali da kuma Nijar.

Kasar ta Habasha ta gamu da rikice-rikicen da suka hada da arangama tsakanin masu zanga-zangar adawa d gwamnati, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane kimanin 500 kamar yadda kungiyoyin kare hakkin adam suka bayyana.

Masu zanga-zangar dai na zargin gwamnatin Habasha da take hakkokinsu ta hanyar kwace filayensu tare da siyar wa kamfanonin kasashen ketare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.