Isa ga babban shafi
Faransa-MDD

Kasashe 30 zasu shiga yarjejeniyar kare muhalli

A Yau laraba, akalla kasashen duniya 30 ne ake saran zasu rattaba hannu kan yarjejeniyar kare muhallin da aka kulla a birnin Paris, a ci gaba da taron Majalisar Dinkin Duniya da akeyi a birnin New York.

Masu rajin kare Muhalli a lokacin zanga zanga a Paris na magance matsalar  gurbatar yanayi.
Masu rajin kare Muhalli a lokacin zanga zanga a Paris na magance matsalar gurbatar yanayi.
Talla

Sanarwar Majalisar ta nuna cewar cikin kasashen da zasu sanya hannun sun hada da manyan kasashen da suka fito daga yankin Latin Amurka da suka hada da Argentina, Brazil da Mexico.

Sauran sun hada Bangladesh, Singapore, Thailand da Daular Larabawa.

Kafin dai yarjejeniyar ta fara aiki, sai kasashe 55 dake haifar da akalla gurbacewar yanayi kashi 55 sun sanya hannu kan yarjejeniyar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.