Afrika ta kudu ta fi Najeriya Karfin tattalin arziki
Afrika ta kudu ta koma matsayinta na kasa mafi girman tattalin arziki a Afrika, bayan doke Najeriya a ma'auni Arzikin kasa duk da matsalolin koma baya da ta ke fuskanta.
Wallafawa ranar:
Dukkannin kasashen biyu sun fuskanci koma bayan tattalin a cikin wannan shekarar. Sai dai yayin da Afrika ta Kudu ta samu tagomashi kan kudin kasar ta da 16 cikin 100 a bana, faduwar darajar Naira a Najeriya ya durkusar da ita sama da kashi 3 na yawan girman tattalin arzikin ta.
A cewar kafar yadda labaran Bloomberg, dake rawaito rahotanni IMF, ma’aunin tattalin arzikin Najeriya a yanzu na kan dala biliyan 296, na Afrika ta kudu kuma na kan dala biliyan 301.
Najeriya dake fuskantar barazanar tattalin arziki irinsa na farko cikin shekaru. A shekara ta 2014 kasar ta kasance kasa mafi girman tattalin arziki a Afrika lokacin da ma ‘aunin tattalin arzikinta ya zarce dala biliyan 500 irinsa na farko a shekaru 20.
A yanzu dai Afrika ta Kudu ta dawo matsayin da Najeriya ta kwace mata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu