An bukaci a kafa dokar ta-baci a Borno saboda yunwa
Kungiyar Agaji ta Medecins Sans Frontieres ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta kafa dokar ta-baci a yankin arewa maso gabashin Najeriya sakamakon matsalar yunwa da ake fama da ita. Kungiyar ta ce mutane da dama ne ke mutuwa sakamakon yunwa, yayin da wasu fiye da dubu 500 ke cikin matsanancin hali a yankin wanda Boko Haram ta daidaita.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Rahoton na kungiyar likitocin MSF ya zo ne a daidai lokacin da tawagar kwamitin kula da ‘yan gudun hijira na majalisar wakilan kasar ya ziyarci garuruwan Damboa da kuma Bama, inda dubban mutane ke cikin matsanancin hali, Wakilin RFI Hausa a Maiduguri Bilyamin Yusuf ya ce Yara da dama ne suka mutu sakamakon cututtuka da yunwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu