Isa ga babban shafi
Najeriya

Ana fama da karancin abinci a Borno

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana fama da tsananin rashin abinci a Yankin Arewa maso Gabashin Najeriya sakamakon rikicin Boko Haram kamar yadda ake fama da yunwa a yankin Darfur na Sudan da kuma Sudan ta kudu da ke ake rikici.

Dubban 'Yan gudun hijirar rikicin Boko Haram ke bukatar taimako a Najeriya da Nijar
Dubban 'Yan gudun hijirar rikicin Boko Haram ke bukatar taimako a Najeriya da Nijar REUTERS
Talla

Jami’in Majalisar da ke kula da aikin jinkai a Yankin Sahel, Toby Lanzer ne ya bayyana haka bayan wata ziyarar aiki da ya kai Yankin.

Lanzer ya ce ya yi aiki a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Darfur da kuma Sudan ta kudu, amma bai taba ganin halin kuncin da mutane suka shiga kamar na kauyukan Jihar Borno ba.

Jami’in ya ce ana bukatar akalla Dala miliyan 220 nan da makwanni 10 domin ceto rayukan mutanen yankin da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.